Majalisar Kaduna ta amince da nadin mataimakin gwamnan jihar

Patrick Yakowa
Image caption Gwamnan Jihar Kaduna, Patrick Yakowa

Majalisar dokokin jahar Kaduna ta tabbatar da zaben Alhaji Mukhtar Ramalan Yero a matsayin mataimakin gwamnan jahar.

A jiya dai bayanai suka nuna cewar gwamnan jahar Mista Patrick Ibrahim Yakowa ya mika sunansa domin dare karagar mukamin mataimakin gwamnan jihar.

Hakan dai ya biyo bayan rantsar da shi Mr Patrick Yakowa wanda a da yake rike da mukamin na mataimakin Gwamna a matsayin gwamnan jihar ta Kaduna.

Korafe korafe da dama ne dai suka biyo bayan zaben na Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, inda wasu a jahar ke cewa ba a yi musu adalci ba, ta hanyar kin la'akari da sashen da ya kamata a baiwa mukamin.