Shugaba Obama ya sanar da sauyi a kan hakar mai

Shugaba Obama
Image caption Har yanzu mai na ci gaba da malala

Shugaba Obama ya ba da sanarwar yin manyan sauye-sauye ga harakar hako mai a cikin teku, bayan tsiyayar man da aka samu a Tekun Mexico.

Ya ce, fiye da komi, wannan bala'in da ya shafi muhalli da tattalin arziki ya nuna bukatar da ke akwai ta gaggawa ta samar da makamashin da ba ya gurbata muhalli.

Shugaban Amurkan ya dakatar da binciken gano mai a karkashin teku har nan da wasu watanni shidda.

Ya kuma jingine gwaje-gwaje a wasu rijiyoyin mai guda talatin da ukku a tekun Mexicon.

Baya ga haka kuma, shugaba Obaman ya soke bayar da karin lasisin hakar mai a cikin teku.