Sabuwar manufar tsaro a Amurka

Sabbin manufofin tsaro a Amurka
Image caption Mai baiwa shugaba Obama shawara kan harkokin tsaro James Logan

Gwamnatin shugaba Obama na shirin kaddamar da wata sabuwar manufa kan harkokin tsaron kasa, wadda za ta fi bada fifiko kan tuntuba, maimakon manufar da aka rika amfani da ita ta taron numfashi a zamanin gwamnatin Bush da ta shude.

Ana kuma sa ran za ta kara tashi haikan wajen sa ido kan abin da ta kira barazanar dakarun sa kai na cikin gida.

Wakilin BBC kan harkokin tsaro Nick Childs, yace kowanne shugaban kasa dai na fito da wani tsari na samar da tsaro a kasar sa.

Wato wata hanya da sojinsa za su yi aiki da ita, da matakan diplomasiyya da kuma sauran tsare tsare akan harkar data shafi tsaro.

Manufar tsarin

Abubuwan da sabon tsarin ya kunsa wanda gwamnatin ta fitar ya jaddada mahimmancin samar da tsaro a bangaren kasashen waje, wani batu kuma daya saba da akalla shekarun farko na abinda gwamnatin Bush tayi.

Sabon tsarin dai ya jaddada mahimmancin alakar dake tsakanin lafiya da tattalin arziki da kuma harkar tsaron kasa.

Kuma ana sa ran cewa za'a dauki karuwar da ake samu a bangaren barazanar ta'addanci ta cikin gida, da ta kasance daya daga cikin abubuwan da za'a fi mayar da hankali akai.

Musamman ma a saboda yunkurin kai hare haren da suka yi ta faruwa a 'yan kwanakin nan, da kuma makarkashiyar wadansu hare haren da aka gano a Amurkan.

Sai dai masu kalubalantar tsarin sun bayyana cewa wannan hanyar ba lallai bane ta samar da abu mai ma'ana, Wala Allah a Iran ko a Korea ta Arewa ko kuma yankin Gabas ta tsakiya.