An sabunta: 28 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 12:25 GMT

An kai mummunan hari a masallatan Pakistan

Hare-haren birnin Lahore na Pakistan

Birnin Lahore ya dade yana fuskantar hare-hare daga masu tada kayar baya

Fiye da mutane tamanin ne suka mutu, bayanda 'yan bundiga suka kai hari a masallatai biyu na mabiya darikar Ahmadiyya a birnin Lahore na Pakistan.

Ana saran adadin wadanda suka rasun zai iya karuwa, adai dai lokacin da ake ci gaba da jin kararrakin bindiga da fashe-fashe a daya daga cikin masallatan.

An kai hare-haren ne a dai dai lokacin jama'a ke halattar sallar Juma'a.

Rahotanni suka ce 'yan sanda sun shiga daya daga cikin ginin, yayinda aka ci gaba da ba-ta-kashi a dayan.

Birnin Lahore ya yi kaurin suna wajen fuskantar hare-hare daga masu tada kayar baya.

Wasu rahotanni na cewa 'yan bindiga na ci gaba da garkuwa da masu ibada a masallaci, a yankin Garhi Shahu.

Daukar mataki

Jami'an 'yan sanda sunce a yanzu su ke da iko da daya daga cikin masallatan, bayanda suka kashe daya daga cikin masu tada kayar baya, sannan suka kama biyu.

 • Hari kan masallatan Pakistan
  Wasu 'yan bindiga sun kai hari a kan wasu masallatan kasar Pakistan cike da masallata a lokacin da ake shirye-shiryen sallar Juma'a. Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
 • Hari kan masallatan Pakistan
  Jami'an tsaro dai sun yi wa yankin kawanya, jim kadan bayan kai harin a kan wasu masallatai na wasu tsirarun mabiya darikar Ahmadiyya a kasar.
 • Hari kan masallatan Pakistan
  'Yan bingar dauke da bindigogi kirar AK-47, kananan bindigogi da gurneti, sun haddasa wata fashewa mai karfi a wajen masallacin, kafin daga bisani su bude wa masallata wuta.
 • Hari kan masallatan Pakistan
  'Yan bindigar sun yi garkuwa da mutane a cikin masallacin, abinda ya sa 'yan sanda suka wahala wajen ceto wadanda suka samu rauni.
 • Hari kan masallatan Pakistan
  A masallacin Garhi Shehu, maharan sun tayar da bam din da yake jikinsu a lokacin da 'yan sanda suka yi kokarin kawo karshen garkuwar da suka yi da mutane.
 • Hari kan masallatan Pakistan
  Daga bisani jami'an tsaro sun samu nasarar kwato masallatan biyu, bayan an shafe sa'o'i da dama ana bata kashi.
 • Hari kan masallatan Pakistan
  Babu tabbas a kan ko suwa suka kai harin a kan mabiya darikar Ahmadiya, wadanda wasu ke ganin sun yi ridda, sai dai jami'ai na ganin da hannun 'yan Taliban a harin.

Wakilin BBC a Islamad, Aleem Maqbool, yace harin yana da alaka da rikicin addini.

Wadanda suka shaida abinda ya faru sun gayawa BBC cewa, maharan sun kai harin ne a lokaci guda a masallatan biyu.

"Suna dauke da bundugogi samfurin AK-47, da kanan bundugogi da gurneti da sauran makamai".

Tuni dai motocin asibiti suka garzaya da gawarwakin wadanda aka kashe dama wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti.

Harin dai na zuwa ne bayanda aka kashe mutane 45 a watan Maris, sakamakon harin bom din da aka kai a wata unguwa mai cike da jama'a.

An dade ana kai hare-hare masu alaka da addini a yankin Punjab dama sauran sassa da dama na Pakistan.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.