Obama ya ziyarci yankunan da tsiyayar mai ta shafa

Obama na duba barnar tsiyayar mai
Image caption Obama na duba barnar tsiyayar mai

Sakamakon sukar da ake masa a baya-bayan nan, shugaba Obama ya kai ziyara ta biyu a Louisiana, domin ganin yadda aikin kwashe man da ya tsiyaya a tekun Mexico ke gudana.

Ya bi gabar ruwa ta jirgin sama domin ganin barnar da tsiyayar man ta janyo, kuma ya kwashe fiye da sa'o'i biyun da aka tsara zai yi a yankin.

Wakilin BBC ya ce, kamfanin BP ne kawai ke da kayayakin aikin da ake bukata, domin hana tsiyayar man.

Kuma doka ta ce Kamfanin na BP ne ke da alhakin kwashe man.

Majalisar wakilan Amirka ta amince a ninka har sau hudu, irin harajin da kamfanonin mai ke biya a cikin wani asusu na ko ta kwana, domin tinkarar irin wannan bala'i na tsiyayar mai.