Taron shugabannin Korea ta Kudu da Japan da China

Shugaban Korea ta Kudu Lee Myung-bak
Image caption Shugaban Korea ta Kudu Lee Myung-bak

Shugabannin Korea ta Kudu da Japan da kuma China, suna gudanar da taron kolinsu na shekara-shekara, inda batun nitsar da wani jirgin ruwan yakin Korea ta Kudu, yake kan gaba a ajandar taron.

Shugaban Korea ta Kudu, Lee Myung-bak, shi ne ke daukar bakuncin taron, wanda ake yi a tsibirin Jeju na kasar.

Korea ta Arewa dai ta musanta cewa ita ke da alhakin kai harin. Ta ce ba ta da ma irin makamin da aka yi amfani da shi wajen kai harin.

Kawo yanzu dai China ta ki ta yi Allah wadai da al'amarin, kuma ba ta fito a bainar jama'a ta dora laifi a kan Korea ta Arewa ba.