Shugaban Malawi ya yafe wa 'yan liwadi

'Yan liwadi a Malawi
Image caption 'Yan liwadi a Malawi

Shugaban Malawi, Bingu wa Mutharika, ya yi afuwa ga wasu 'yan luwadi biyu da aka yankewa hukuncin daurin shekaru 14 a kurkuku a makon jiya, a shari'ar da ta janyo fushin wasu kasashen duniya.

Shugaba Mutharika ya ce mutanen biyu sun aikata laifi na bata sunan al'adu da addini da kuma dokokin kasar ta Malawi, amma ya yafe ma su bisa dalilan jin kai.

Ya bada sanarwar ce, bayan ya gana da babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki-Moon, wanda ke ziyara a kasar.

Sakataren yayi marhabin da wannan mataki, yana mai cewar zai yi kamfe na ganin an soke dokar da ke hukunta 'yan luwadi a Malawi.