Tsawa ta kashe mutane a kasar Guatemala

Kimanin mutane goma sha biyu sun mutu a kasar Guatemala sakamakon wata tsawa mai dauke da ruwan sama.

Daruruwan mutane ne kuma suka bar gidajensu sakamakon tsawar wadda ta jefa kasar cikin rudani.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya na cikas ga yunkurin kai agaji inda aka rufe babban filin jirgin kasar

A baya dai kasar Guatemala ta yi fama da bala'i daban-daban sakamakon aman wutar da duwatsunta su ka yi,da kuma ambaliyar teku.