China ta bullo da sababbin dokokin hana yansanda gana akuba

Wani Dansanda gaban shari'a kan azabtarwa a china
Image caption Wani Dansanda gaban shari'a kan azabtarwa a china

China ta wallafa sababbin dokokin dake da nufin hana yansanda yin amfani da azabtarwa domin neman amsa aikata laifi.

Yunkurin ya biyo bayan fushin da aka nuna game da wani lamari wanda wani mutum ya kashe shekaru gomaa gidan kaso saboda kisan kan da aka gana masa azabar amsa aikatakawa.

Tuni dai akwai dokokin dake hanin gana akuba, to amma masu aiko da labarai sunce ana matukar yin watsi da su, kuma azabtarwa wani abune da ya zama ruwan dare a gidajen yarin China.

Sababbin dokokin na nufin cewar China na son ta inganta tsarinta na shari'a ne, musamman wajen shari'o'in da suka shafi hukuncin kisa