An sabunta: 31 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 15:15 GMT

Isra'ila ta kashe masu fafutika kan Gaza

 Masu zanga zangar la'antar Isra'ila a Santanbul

Masu zanga zangar la'antar Isra'ila a Santanbul

Sojin kundunbalar Isra'ila sun afkawa wani jerin gwanon jiragen ruwa dauke da daruruwan masu fafutikar goyon bayan Palasdinawa dake kokarin kai kayan agaji zuwa zirin Gaza a wata bijirewa toshiyar da Isra'ila ta yiwa yankin.

Sojin Isra'ila sunce masu fafutika akalla goma ne aka kashe sannan an jiwa sojoji 6 rauni bayan da suka hau jiragen ruwan ta hanyar amfani da helikwabtoci. Akwai dai rahotannin dake sabawa juna game da abunda ya faru.

Yan Isra'ila na cewar an kaiwa sojojin kundunbalarsu hari ne a lokacin da masu fafutikar suka kwace wata bindiga daga daya daga cikin sojojinsu sannan ska bude wuta.

Wadanda suka shirya lamarin kuma sunce dakarun Isra'ila sun soma harbi ne da hawansu cikin jiragen ruwan.

 • Sojin Israila a kan jirgin ruwan agaji
  Sojin kundunbalan Israela sun yi dirar mikiya a kan wasu jerin gwanon jiragen ruwa shida na masu fafutuka dake ke kokarin karya lagon toshiyar da Israela ta yi wa al'ummar Gaza na Palasdinu.
 • Wadanda suka jikata
  Sojin Israela sun ce akalla masu fafutuka goma ne suka rasa rayukansu yayinda sojin kundunbala shida suka samu raunuka a lokacin da suka afka wa jiragen ruwan.
 • Jiragen Saman da aka yi amfani da su
  Sojojin Israela sun yi amfani da jiragen sama wajen yin dirar mikiya a kan jerin gwanon jiragen ruwan.
 • Mace dauke da gadon daukar marasa lafiya
  A nan za a iya ganin wata mace dauke da gadon daukara marasa lafiya da ya baci da jini a cikin jirgin ruwan.
 • Sojin Israela sun kama mai fafutuka
  Sojojin Israela sun ce masu fafutukar sun yi harbi suka kuma kai musu hari da wukake da gatari. Su kuwa masu fafutuka sun ce sojin Israelan sun bude wuta ne ba tare da an tsokane su ba.
 • Masu zanga zanga na kona tutar Israela
  Mutane da dama ne suka yi ta zanga zanga a sassa daban daban na duniya domin yin Allah wadai da matakin kisan da sojin Israela suka yi.
 • Sojin Israela na jan jiragen ruwan zuwa gaba
  Israela ta dauki matakin janye jiragen ruwan agajin zuwa gabar ruwanta na Ashdod, inda ta ce za ta tasa keyar mutanen dake ciki su bar yankin
 • Jiragen ruwan agaji
  Jiragen ruwan agajin sun bar gabar ruwan kasar Cyprus ne ranar Lahadi, kuma ana sa ran isarsu can ranar Litinin dauke da kayayyakin agaji da suka kai ton 10,000.

Lamarin dai ya faru ne a cikin ruwayen kasa da kasa.

Kasashen duniya dai sun yi matukar Allah wadai da matakin da Isra'ilar ta dauka a kan jerin gwanon jiragen ruwan, musamman ma kasar Turkiya,inda galibin masu fafutikar dake cikin jiragen ruwan suka fito.

Kasar ta Turkiya ta kira Jakadanta dake a Tel Aviv, sannan kuma ana gudanar da gagarumar zanga zanga a Santanbul.

Kasar Girka kuwa ta janye wani atisayen soji da ta shiryi yi tare da Isra'ila.

A Washington kuma Fadar White House ta ce Amurka ta yi matukar jin takaici game da asarar rayukan da aka samu da kuma jikkatar wasu mutanen a lamarin.

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki -Moon ya ce ya kadu da lamarin,yayinda kuma Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ya bayyana shi da cewar wani kisan kiyashi ne.

A baya dai sojojin Isra'ila sun ce za su kai jirgin ne tashar jiragen ruwansu, inda za su sauke masu kare hakkin bil adaman da ke cikin sa don su koma da su gida.

Israi'la ta ce tana bari a shiga da kimamin tan dubu goma sha biyar na kayayyakin agajin zuwa yankin Gaza a duk mako.

Sai dai majalisar dinkin duniya ta ce wannan bai kai adadin da ake bukata ba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.