Isra'ila ta tsare jirgin ruwan Palasdinu

Shugabannin Hamas sun ce sojojin Isra'ila sun kama jirgin ruwansu da ke dauke da kayayyakin agaji, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa yankin Gaza.

Sai dai ba a tabbatar hakan ba,sannan kuma ba bu wanda ya sani ko an yi taho-mu-gama sakamakon kama jirgin.

Sojojin Isra'ila sun ce ba za su ce komai akan batun ba,amma BBC ta fahimci cewa sau da dama ne sojan ruwan suka umarci matuka jirgin su koma da kayan amma su ka ki.

An rasa duk wata hanya da za a yi magana da matuka jirgin.

A baya dai sojojin Isra'ila sun ce za su kai jirgin ne tashar jiragen ruwansu, inda za su sauke masu kare hakkin bil adaman da ke cikin sa don su koma da su gida.

Israi'la ta ce tana bari a shiga da kimamin tan dubu goma sha biyar na kayayyakin agajin zuwa yankin Gaza a duk mako.

Sai dai majalisar dinkin duniya ta ce wannan bai kai adadin da ake bukata ba.