Mutum ashirin da biyar sun mutu a Mexico

Hukumomin 'yansanda a kasar Mexico sun ce sun gano wasu gawawwakin mutane ashirin da biyar a wani tsohon wajen hakar ma'adanan kasar da ke birnin Guerrero.

Hukumomin sun ce bisa ga dukkan alamu,an yi ta jibge gawawwakin ne a lokuta daban-daban a wajen hakar ma'adanan da ke kusa da wani fitaccen wuri da akan je yawon bude ido.

Sai dai 'yansandan sunce suna kyautata zaton gawawwakin na masu shan miyagun kwayoyi ne.

Birnin Guerrero dai ya yi kaurin suna wajen fadace-facen da ke da nasaba da masu harka da miyagun kwayoyi