Najeriya za ta ceto kamfanonin jiragen samanta

Jirgin saman kamfanin Virgin

Babban bankin Najeriya ya ce zai bayar da naira bilyan 500 domin ceto kamfanonin jiragen saman kasar.

Kudaden tallafin da aka fara sanar da ware su a watan Maris, asali an ware su ne domin bunkasa sassan masana'antu da samar da wutar lantarki na kasar.

Sashen hada-hadar jiragen saman kasar wanda yake fama da tsadar kudaden man jirgi, ya samu habaka sosai a 'yan shekarun nan, sai dai kamfanonin sun ci bashi har wuya.

A watan Agustan shekarar 2009, babban bankin Najeriya ya samar da naira bilyan 400 don ceto wasu bankunan kasar.

Kaucewa Matsala

"Kamfanonin jiragen saman a yanzu za su iya shiga a dama da su a kudaden tallafin, kuma wadanda suka ci bashin banki a yanzu za su iya sabunta bashin nasu har tsawon shekaru goma zuwa sha biyar" in ji mai magana da yawun bankin Mohammed Abdullahi.

Ya kuma kara da cewa, hakan zai kawar da yiwuwar samun matsalar kudade a sashen na hada-hadar jiragen saman kasar.

Kamfanin jiragen saman Virgin Atlantic ya ce yana shirin sayar da kaso 49 cikin dari da ya mallaka a kamfanin Nigeria Eagle Airlines, wanda a da ake kira Virgin Nigeria.

A shekarar da ta gabata ne dai, kamfanin ya dakatar da zirga-zirgarsa ta zango mai tsawo zuwa Birtaniya da kasar Afrika ta Kudu, wadanda suke janyo masa asara, domin mayar da hankali kan zirga-zirga a cikin gida.