An sabunta: 1 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 13:44 GMT

Mata masu sana'ar 'sukola' a kudancin Najeriya

mata masu sanar wanki da guga

A Najeriya, kuncin rayuwa da matsalar rashin aikin yi ko jarin kama wata sana’a, ba wai ga maza kadai abin ya tsaya ba, al’amarin ya shafi mata musamman ma a yankin arewacin kasar, inda wani rahoton majalisar dinkin duniya ya nuna cewa, jama’ar yankin sun fi fama da matsalar talauci fiye da mutanen kudancin kasar.

A sakamakon haka ne wasu daga cikin matan arewacin Najeriyar suke tafiya ci-rani yankin kudu maso gabashin kasar, inda sukan yi ’yan sana’o’i ciki kuwa har da sana’ar wankin tufafi, domin su sami abin rufa wa kansu asiri.

Sau tari akan ce aikin maza na maza ne, kuma sana’ar sukola ko wankin tufafi tana daya daga cikin sana’o’in da ake yi wa irin wannan kallo.

 • Wanki matan arewa
  A Najeriya, kuncin rayuwa da matsalar rashin aikin yi ya sanya wasu matan arewacin Najeriyar suna tafiya ci-rani yankin kudu maso gabashin kasar, inda suke sana’ar wankin tufafi.
 • Shanya
  Sau tari akan ce aikin maza na maza ne, kuma sana’ar sukola ko wankin tufafi tana daya daga cikin sana’o’in da ake yi wa irin wannan kallo.
 • sana'ar wanki da guga
  Ko me zai hana matan su yi zamansu a gida su rika gudanar wasu sana’o’i, maimakon zuwa Enugu domin sana’ar wanki? Nan dai wata mata ce mai suna Rakiya ta iso bakin rafin Ezu da kayan wanki.
 • mata masu wanki da guga
  Wata mata mai suna Maman-godiya tana wankin tufafi a gabar rafin Ezu da ke kan babbar hanyar Enugu zuwa Anaca (Onitsha)
 • Mata masu sana'ar wanki
  Wakilinmu a Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed a lokacin da yake hira da Maman-godiya, daya daga cikin matan arewacin Najeriya da ke sana’ar sukola a kudancin Najeriya.
 • Mata masu sana'ar wanki da guga
  Wasu matan arewacin Najeriya suna sana’ar wanki a gabar rafin Ezu da ke kan babbar hanyar Enugu zuwa Anaca (Onitsha).

To, amma a yanzu wasu mata da kan zo ci-rani nan yankin kudu maso gabashin Najeriya daga arewacin kasar, don neman na-kai ko abin yi, su ma sun rungumi wannan sana’a gadan-gadan, kuma suna gudanar da ita ba kama hannun yaro.

Waka a bakin mai ita

To, da yake masu iya magana kan ce, waka daya ba ta gama nika, wakilinmu Abdusssalam Ibrahim Ahmad ya bulla wani waje inda matan na arewacin Najeriya sukan gudanar da wannan sana’a ta wanki yau da kullum inda ya tambayi wata mata mai suna Lami, ko yaya suke gudanar da sana'ar?

"Muna wanke zannuwa, da wanduna".

Ita ma wata matar mai suna Lamin, ta shaida wa Abdussalam dalilinta na rungumar wannan sana'ar:

"Ba ni da kudi, ba ni kuma da wata sana'a shi ya sa na zo nake wannan sana'ar ta wanki. Muna samun kamar dari biyu zuwa uku a yini."

Wata tambaya da ke wadari game da batun fitowar wadannan mata ci-rani daga arewacin Najeriya ita ce, shin me zai hana su yi zamansu a gida su rika gudanar wasu sana’o’i, maimakon su niki gari su nufi Enugu domin sana’ar wanki? Wata mata mai suna Rakiya, daga cikin wadannan mata da ke zaune a kasuwar shanu ta Ugwuoba a jihar Emnugu, cewa ta yi:

"Idan ba ka da shi, kana son ka yi sana'a, dole ka fito nema, idan ka samu sai ka je gida ka nutsu ka yi sana'arka da kudaden da ka samo a waje".

Sana'ar maza

To ko matan ba su ganin wannan sana'ar ta maza ce saboda wahalar da ke cikinta? Rakiya watan mata ce da ita ma take irin wannan sana'ar ta Sukola:

"Hakan nan muke kokari muke yin wannan sana'ar. Muna kuma amfani da sandar sabulu, da garin sabulu da kuma brush, duk inda ya yi datti sai mu kama mu goge shi da shi. Sai dai sana'ar na shafar lafiyarmu, ko kwanakin nan ma na yi rashin lafiya, saboda yawan dukawa da kuma gajiya." In ji Rakiya wata mai sana'ar wanki da guga a Enugu.

Mafi yawan-yawan wadannan mata dai da aurensu, har ma suna da ’ya’yaye, kamar yadda Rakiya ta bayyana.

Maman-Godiya, uwar wasu yara uku wadda ita ma ta baro biyu daga cikinsu gida arewa, ta yi amanna cewa, baro yaran wani abin damuwa ne, saboda yadda hakan ke shafar rayuwar yaran.

Akan ce, uwa mai maganin kukan ’ya’yanta. To, sai dai ko yaran da iyayen nasu mata kan taho da su ci-rani, su ma suna fuskantar matsaloli da dama.

Fatan ire-iren wadannan mata na arewacin Najeriya dai shi ne, su rika samun tallafi gwaggwaba, don su kama kwararan sana’o’i ko harkokin kasuwanci su sami hanyar dogaro da kansu.

Ta hanyar bayar tallafi na hakika ta fuskar sana’o’i ga matan na arewa, musamman ma wadanda ke yankunan karkara, tabbas zai yanke masu matsalar zaman kisan dabe, da irin wannan ga-ludayar fita ci-rani da ya kuma kawar masu da talauci.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.