Kungiyar tsaro ta NATO tayi tur da farmakin Isra'ila

Anders Fogh Rasmussen
Image caption Sakataren kungiyar tsaro ta NATO

Matsin lambar diflomasiyya na karuwa akan Isra'ila, kwana daya bayan sojin kundunbalarta sun afkawa jiragen ruwan dake kokarin keta datsewar da ta yiwa Gaza.

Sakatare Janar na Kungiyar tsaro ta NATO, Anders Fogh Rasmussen, ya yi Allah wadai da asarar rayukan da aka samu a lokacin farmakin, sannan ya bukaci da a gaggauta sakin jiragen ruwan da kuma fararen hulan da Isra'ilar ke tsare da su.

Masu fafutikar goyon bayan Palasdinawa akalla tara ne aka kashe, kuma hudu daga cikinsu 'yan kasar Turkiyya ne.

Turkiyya ta kira farmakin a matsayin wani "mummunan kisan kiyashi" wanda kuma dole ne a yi hukunci a kansa.