Wata kotu a London ta sami Christine Ibori da laifin halalta kudin haram

Mutum mutumin kotu
Image caption Kotu ba sani ba sabo

Masu taya alkali yanke hukunci a wata kotu dake London sun sami Christine Ibori 'yar'uwa ga tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori, da laifin halalta kudin haram da kuma sama da fadi da kudade kimanin dalar Amurka sama da miliyan dari.

Kotun ta ce Christine wacce aka tuhuma da laifuka goma sha biyu ta taimakawa dan'uwanta James Ibori wajen zambatar kudin daga asusun jihar Delta zuwa asusun wani banki dake London.

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC a Najeriya na zargin tsohon gwamnan da sama da fadi da dalar Amurka kusan miliyan dari uku.