Shugaba Jonathan ya nemi a zaftare kasafin kudin bana

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya ya aikewa majalisar dokokin kasar da wasika ta neman zaftare kasafin kudin bana

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya bukaci majalisar dattawa ta kasar da ta duba yiwuwar rage yawan kasafin kudin kasar na wannan shekarar.

A cikin wata wasika da ya aike wa majalisar, Shugaban kasar ya nemi majalisar da ta yi la`akari da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya domin rage yawan kasafin kudin.

Masana dai na cewa kasar na da zabin rage kasafin kudin nata ta hanayr rage kudin ganagan danyen mai daga dala67 zuwa 55, ko kuma rage darajar naira.

Anyi kasafin kudin kasar na bana ne kan kowane gangan danyen mai za'a saida shi akan dalar Amurka 67, kuma kasafin baki dayanshi ya tashi akan naira trillion hudu da digo shida.