Jagoran Al-Qaeda a Afghanistan ya rasu

Mustafha Abu Yazid
Image caption Mustafha Abu Yazid na daga cikin shugabannin Al-qaeda

Rahotanni na nuna cewa daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar Al-Qaeda a kasar Afghanistan ya rasu, sai dai babu wani cikakken bayani kawo yanzu.

Wani shafin intanet na Islama ya rawaito wata sanarwa da al-Qaeda ta fitar na cewa Mustafa Abu al-Yazid, wanda kuma aka sani da Sheikh Said al-Masri ya rasu, tare da matarsa, da yaransa guda ukku da wasu mutanen da kuma mata da yara kanana.

A daidai wannan lokaci kuma, mahukuntan Amurka a Washington na cewa, sun yi imanin cewa mutumin ya rasu a wani yankin kabilu a Pakistan, wanda jiragen Amurka masu sarrafa kansu ke yawan kaiwa hari.

Wakilin BBC ya ce, hukumomin Amurkar na cewa idan dai da gaske ne ya rasu, babbar nasara ce, to amma rahotanni a baya dangane da rasuwar ta sa, sun kasance ba gaskiya ba.