Shugaba Sarkozy ya bukaci a baiwa Afrika dama

Shugaba Sarkozy na Faransa
Image caption Faransa na neman karfafa dangantakar kasuwanci da Afrika

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, ya nemi da a baiwa nahiyar Afrika karin damar fada aji a duniya, da kuma kujerar din-din-din a Kwamitin sulhu na majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban na magana ne a wajen taron kwanaki biyu da ake gudanarwa tsakanin nahiyar ta Afrika da kasar Faransa, a birnin Nice na Faransar.

Yace nahiyar ka iya taka mahimmiyar rawa wajen ci gaban duniya baki daya.

Sannan ya yi alkawarin neman kawo sauyi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya badi. Shugannin kasashe talatin da takwas da kimanin 'yan kasuwa 200 ne ke halattar taron, wanda shi ne na farko da Mista Sarkozy ke daukar nauyi.

"Babu wata matsala da ke addabar duniya da za a iya shawo kanta ba tare da taimakon nahiyar Afrika ba," inji mista Sarkozy.

Amincewa ko rashin ta

Shugabannin sojin Nijar da Guinea, na daga cikin wadanda ke halattar taron, kuma hakanne ya janyo korafi daga shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma.

"Gayyatar su na nufin amincewa da su, domin haka muke fassarawa a nan," a hirar sa da gidan talabijin na France 24.

Ba'a dai gayyaci Madagascar ba wacce ke fama da rikicin siyasa, yayinda Zimbabwe taki tura wakilai bayanda aka ki amincewa da kasancewar shugaba Robert Mugabe.

Faransa wacce ke gogayya da China da sauran kasashen duniya domin neman kasuwanni a Afrika, na amfani da taron domin bunkasa huldar kasuwancin da kasashen nahiyar.