Taron jin ra'ayin jama'a kan kundin zaben Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption An dade ana zargin aikata magudi a zabukan Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya, za ta gudanar taro a bainar jama'a dangane da gyara ga kundin zaben kasar, domin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

Jam'iyyu da kungiyoyin dake sha'awar halarta, ana sa ran za su kasance a majalisar dokokin kasar dake Abuja.

An yi ta ikirarin cewa, zabukan da suka wakana a shekarun 2007 da 2003, an tabka magudi sosai a cikinsu, kuma a farkon badi ne ake sa ran za a gudanar wani babban zabe a kasar.

Shugaban Nigeria Dr Goodluck Jonathan, ya ce zai bayyana sunan sabon shugaban hukumar zaben kasar a wannan mako, to amma masu gwagwarmaya kan dimokradiyya sun ce, bai kamata shugaban kasa ne ke da ikon nada wannan mukami ba.

Batun gyara kundin zaben kasar dai ya dade yana janyo cece-kuce tsakanin 'yan siyasa da kungiyoyin kwadago da masu fafutukar dimokradiyya a kasar.