An kai hario wajen taron sulhun Afghanistan

Harabar taron Jirga wanda aka kaiwa hari
Image caption Harabar taron Jirga wanda aka kaiwa hari a Afghanistan

Wasu da ake zargin 'yan bunduga ne sun kai hari kan taron sulhu na "jirgi" da shugaba Hamid Karzai yake budewa a birnin Kabul.

Rokoki uku aka harba a kusa da wurin taron. Jami'ai suka ce an kashe maharan biyu, yayinda aka kama daya.

Shugaba Karzai na fatan yin amfani da taron na "jirga" domin tayin tallafin tattalni arziki ga mayakan Taliban.

Shugabannin Taliban sun yi Allah wadai da taron, sannan suka yi barazanar kashe mahalatta taron. Karar bashewar rokoki ta kawo tsaiko ga jawabin bude taron da shugaba Karzai ya yi.

Ya gayawa mahalatta taron cewa: " Wani na kokarin kawo mana hari da roka....Amma kada ku damu, bara mu ci gaba".

Rawar shugabannin Gargajiya

Kimanin wakilai 1,600- da suka hada da shugabannin kabilu da na addini da 'yan majalisar dokoki daga sassa da dama na kasar ne suka hallara.

Wakilin BBC yace manufar taron itace ta karfafa guiwar shugaba Karzai, amma ana ganin rikici ba zai kare ba muddum ba a cimma yarjejeniya da kungiyar Taliban ba.

Shugaba Karzai ya yi kira ga Taliban, yana mai cewa halayyar su ce ke ci gaba da zaunar da dakarun kasashen duniya a Afghanistan.

"Ya kamata ku bada dama ga dakarun kasashen waje su fice daga kasar mu," inji shugaba Karzai.