An soki matakin Libya na kisan 'yan Najeriya

Shugaban Libya Muammar Gaddafi
Image caption Shugaban Libya ya dade yana kira da a hada kan nahiyar Afrika

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta yi Allah wadai da matakin da Libya ta dauka na kisan mutane 18, ciki harda 'yan Najeriya.

Mutanen 18, wadanda suka fito daga kasashen Chadi da Najeriya da Masar, an kashe su a ranar Lahadi a biranen Tripoli da Benghazi, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ce.

Amnesty International tace tana tsoron cewa mai yiwuwa mutanen ba a yi musu shari'a cikin adalci ba.

An samu mutanen da laifin kisa, sannan aka kashe su ta hanyar harbi, a cewar jaridan Cerene ta Libya.

"Muna tsoron cewa ana yanke hukuncin kisa a Libya, bisa tsarin dokar da bai yi daidai da tanadin kasashen duniya ba," kamar yadda sanarwar da kungiyar ta fitar ta kara da cewa.

Ko a ranar Talata sai da wasu 'yan kasar Nijar dake jiran hukuncin kisa a Libya, suka shaidawa BBC cewa ana cin zarafin su a gidan yarin da ake tsare da su.

'yan kasashen waje ba sa samun adalci a tsarin shari'ar Libya, inji Amnesty.

Image caption Jama'a da dama ne ke shiga Libya domin tsallakawa zuwa Turai

Kisan 'yan kasashen waje da dama

Ana tunanin ba sa samun damar daukar lauya, sannan ba sa fahimtar yadda shari'ar ke gudana domin ba a fassara musu daga harshen Larabci.

A cewar Amnesty, Libya ta kashe 'yan kasashen waje da dama.

Dubban 'yan kasashen waje ne ke tsallakawa zuwa yankin sahara domin fatan shiga nahiyar Turai wata rana. Kuma da dama daga cikin su kan rasa rayukan su, sakamakon yunwa da kuncin rayuwa.

A wasu lokutan sukan rasa rayukan na su ne sakamakon rufewar da sahara kan yi musu.