Majalisa ta cimma daidaito kan tsarin mulki

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption Majlisar dokokin Najeriya zata mika kundin tsarin mulkin da ta yiwa gyara ga majalisun jihohi.

A zaman da ta yi a yau, majalisar dattawan Najeriya ta amince da gyare-gyare ga wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar da suka shafi harkokin zabe.

Ana sa ran cikin makon nan ne za a mika wa majilisun dokokin jihohi talatin da shida dake kasar domin su amince da gyare-gyaren da majalisun dattawa da na wakilai suka samu daidaito akai.

Rahotanni dai na cewa, tuni gwamnonin jihohin suka bada tabbacin cewa, majalisun dokokin jihohinsu zasu amince da kundin da majalisar dokoki ta kasa zata mika musu.

A ciki da wajen Najeriya dai wasu na da ra'ayin cewar, yin zabe cikin gaskiya da adalci ya ta'allaka ne ga yin gyare-gyare ga wasu sassan kundin tsarin mulkin a kan lokaci.