Banki Moon ya nemi Israila ta cire shingenta

Sakatare na majalisar dinkin duniya Ban Ki- Moon
Image caption Sakatare na majalisar dinkin duniya Ban Ki- Moon

A lokacinda yake bayani dangane da mummunan harinda Israela ta kai akan tawwagar masu kai agaji zuwa Gaza, Sakatare janar na Majalisar dinkin duniya Mista Ban Ki-Moon, ya bukaci Israela da cewa ba tare da bata lokaci ba, ta janye datsewar da take wa Gaza.

Mista Ban ya bayyana shekaru ukku da ta yi tana datse zirin da cewa bai biya bukata ba, kuma ba za ta iya ci gaba da yin haka ba sannan kuma yace abune da bai kamata ba.

Ya ce wannan abin bakin cikin da ya auku, ya fito da matsalar ce fili. Dadewar da aka yi ana datse iyakokin Zirin Gaza, bai biya bukata ba, kuma ba za a iya ci gaba da yin haka ba, sannan bai kamata ba. Dole ne yace hukumomin Israila su janye ba tare da bata lokaci ba.

sakataren na majalisar dinkin duniya ya shafe kusan gabakidaya ranar yana ganawa tare da mambobin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da kuma wakilan kasashen Turkiyya da israila.

Matsalar dai itace wasu mambobin kwamitin sulhun kamar su Turkiya sun hakikance akan cewar lallai sai an gudanar da binciken kasa da kasa kan wannnan batu