Libya zata kashe 'yan Ghana bakwai

Shugaban Kasar Ghana, John Atta Mills
Image caption Masu jiran hukuncin kisan a Libya na neman dauki daga Ghana

Rahotannin dake fitowa daga kasar Libya sunce a gobe ne za a aiwatar da hukuncin kisa kan wasu 'yan kasar Ghana su bakwai bayan da aka aiwatar da hukuncin kisan kan wasu 'yan Ghanar su ashirin a ranar Litinin da ta wuce.

Batun hukuncin kisan a kan 'yan Ghanan na zuwa ne, kwanaki kadan bayan da hukumomin kasar ta Libya suka aiwatar da hukuncin kisa a kan wasu 'yan Nijar ta hanyar bindigewa, lamarin da yayi ta janyo ka ce nace.

Wadanda ke jiran hukuncin kisan dai na korafin cewa an yanke musu hukuncin ne ba tare da sun aikata laifin da ake zargin sun aikata ba.

Wani dan kasar dake cikin wadanda ke zaman jiran aiwatar da hukuncin kisan a kansu ya shaida ma wata jarida mai zaman kanta dake Accra cewa matukar gwamnatin Ghanar ta kasa yin wani abu don ceto rayukansu, to fa a gobe bakin alkalami zai bushe.