Kara kan batun aiwatad da dokar 'yancin kananan yara a Nijeriya

Sanata Ahmed Sani Yarima
Image caption Sanata Ahmed Sani Yarima

Majalisar koli ta harkokin shari'ar Musulunci a Najeriya ta shigar da kara gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja, inda take kalubantar aiwatar da dokar 'yancin kananan yara da Majalisar dokokin kasar ta amince da ita, a shekarar 2003.

Cikin wadanda Majalisar koli ta harkokin shari'ar Musuluncin ke kara sun hada da hukumar kare yancin 'dan Adam ta kasa da shugaban Majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya.

An shigar da wannan kara ce a daidai lokacin da ake ci gaba da cecekuce a Nijeriya, game da auren da Sanata Ahmad Sani, tsohon gwamnan jihar Zamfara yayi, wanda ake cewar shekarun yarinyar ba su wuce goma sha uku ba, shi kuma yake cewar shekarunta sun zarta hakan.

Wannan batu dai ya janyo cece-kuce har ma da kafa wani kwamiti a majalisar dattawa domin binciken lamarin.