A binciki kisan Chebeya, inji Mista Ban

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon
Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya yi kiran a yi bincike mai zurfi kan kisan Floribert Chebeya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta binciki kisan da aka yiwa wani mai fitaccen mai fafutukar kare hakkin bil-Adama.

Babban Sakataren Majalisar ta Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, ya bukaci a yi bincike mai zurfi a kan mutuwar mai Floribert Chebeya, wanda aka tsinci gawarsa a Kinshasa ranar Laraba.

Wannan kiran na Mista Ban ya biyo bayan bukatar da kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suka yi ne na gwamnatin kasar ta Congo ta kafa wata hukuma wadda za ta kunshi jam'ian gwamnatin, da na Majalisar Dinkin Duniya da ma wakilan al'ummar kasar.

Kwamishiniyar kare hakkin bil-Adama ta Majalisar, Navi Pillay, ta yi bayyana cewa Mista Chebeya ya sha fuskantar barazanar kisa da dauri a shekaru ashirin da suka gabata.

Wani babban mai bincike na Majalisar ya ce yanayin kisan Mista Chebeya na nuna alamun cewa gwamnati ce ke da alhaki.

Sai dai har yanzu gwamnatin Congon ba ta ce komai a kan batun ba.

Ranar Alhamis ne dai aka kyale mutum biyu daga cikin iyalan Mista Chebeya, da jami'an Majalisar Dinkin Duniya uku, da kuma wasu mambobi biyu na kungiyar kare hakkin bil-Adaman da ya kafa, mai suna Voice of the Voiceless, suka ga gawarsa a dakin ajiye gawarwaki na Kinshasa.