Wuta ta lashe unguwa a Bangladesh

Gobarar Dhaka, bangladesh
Image caption Fiye da mutane dari ne suka rasa rayukansu a gobarar

Akalla mutane dari da takwas ne suka rasa rayukansu bayanda gobara ta lashe wani rukunin gine-gine a wani yanki mai cunkoson jama'a a Dhaka, babban birnin kasar Bangladesh.

Ko da yake an samu nasarar kashe gobarar, ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu, yayinda masu aikin ceto ke kutsa kai cikin burbushin gidajen da gobarar ta lalata don lalubo karin gawarwaki.

Gobarar dai ta yadu ne cikin hanzari ta mamaye wadansu gidajen kwanan jama'a guda shida; don haka mutanen da ke cikin benayen ba su samu damar tserewa ba.

Sai da 'yan kwana-kwana suka sha wahala matuka kafin su iya shawo kan gobarar saboda karfin harshen wutar da kuma saurin yaduwarta.

Haka nan kuma da kyar 'yan kwana-kwanan suka iya kai kayan kashe gobara wurin da wutar ta tashi wanda ke cikin tsohon birnin Dhaka.

Tsohon birnin dai mai cike da tarihi shi ne tsakiyar birnin mai cunkoso matuka, da kuma lungunan da mota ba ta iya bi.

Gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar wata tranformer ta wutar lantarki, sannan wutar ta fantsama zuwa shagunan da ke kasan benayen inda aka ajiye wadansu sinadarai.

Da yawa daga cikin wadanda abin ya rutsa da su dai suna halartar wata liyafar aure ne a saman daya daga cikin benayen.

Wani wanda ya shaida faruwar al'amarin ya bayyana cewa: “Wannan ginin cike ya ke da sinadarai, akwai kuma kusan ma'aikata dari da hamsin a ciki.

“Sannan ana buki a daya daga cikin gidajen—bukin kuma ya samu halartar mutane da dama; ina kuma kyautata zaton duk sun mutu”.

Sai dai amaryar da ake bikin auren nata, wadda ta bar wurin bikin na dan wani lokaci, ta tsira.

Fiye da mutane dari ne wadanda suka kokkone ko kuma suka yi rauni aka garzaya da su asibiti.

Tashin gobara dai ba bakon al'amari ba ne a birnin na Dhaka wanda ke cikin biranen da suka fi cunkoson jama'a a duniya, to amma wannan ce gobara mafi muni a shekaru da dama.

Mutanen birnin da dama dai na zaune ne a benayen da ba su da kayan kashe gobara kuma ba su da hanyoyin tserewa idan gobarar ta tashi.