Wata babbar jami'ar Tarayyar Turai na ziyara a Nijer

Wasu mata da ke fama da yunwa a Nijer
Image caption Wasu masu fama da yunwa a Nijer

Kwamishiyar Tarayyar Turai mai kula da ayyukan jin kai, Kristalina Georgieva tana wata ziyara a Jumhuriyar Nijar.

Makasudin ziyarar ta yini biyu ita ce fahimtar halin da ake ciki a kasar dangane da batun karancin abinci da ake fama da shi a wasu sassan kasar.

Yanzu haka dai Mrs Georgieva din tana jihar Maradi, inda ta ziyarci yankunan Gidan Roumji da Aguie, wasu daga cikin yankunan da matsalar ta fi shafa.

Tarayyar Turai dai tana daga cikin kungiyoyin da suka amsa kiran da gwamnatin kasar ta Nijer ta yi a cikin wartan Maris na neman agaji daga kasashen duniya domin tinkarar matsalar ta karanci abinci a kasar, sakamakon rashin kyaun daminar da ta gabata.

An shirya nan gaba a yau za ta gaana da Pira ministan kasar, Dr Mahamadou Dandah, sannan kuma ta kira wani taron manema labarai.