Matsin lamba yasa Obama dage balaguro zuwa Asiya

BP yace ya kashe makudan kudade domin hana mai kwarara
Image caption BP yace ya kashe makudan kudade domin hana mai kwarara

A karo na biyu matsil lamba yasa shugaba Barrack Obama ya dage ziyarar da ya tsara kaiwa zuwa kasashen Indonesia da Australia.

Matsin lambar na karuwa ne bayan da malalar da mai ke ci gaba da yi a gabar tekun Mexico taki-ci-taki-cinyewa, bayan shafe makonni shida.

Ana saran shugaban zai kara ziyartar yankin a ranar Juma'a, domin sake ganewa idanunsa irin illar da malalar man ta haifar.

Mista Obama wanda ke magana cikin fushi ya nuna bacin ransa da halayyar kamfanin da ya haifar da matsalar wato BP.

Shugaban kamfanin BP yace zai kira taron masu hannun jari a kamfanin domin duba irin asarar da wannan lamari ya haifarwa da kamfanin.

Alhakin abinda ya faru

Tuni dai fadar White House ta aika da wani daftari dake neman kamfanin BP ya dauki alhakin wani bangare na asarar da abin ya haifar.

A ranar Alhamis ne kamfanin yace ya fara samun nasara a yunkurin da yake yi na dakatar da malalar man, wacce ke ci gaba da tayarwa da jama'a hankali a kasar.

Kamfanin BP yace kawo yanzu ya kashe sama da dala biliyan guda domin shawo kan matsalar.

Sai dai jami'an gwamantin Amurka sun ce nasarar da kamfanin ke ikirarin samu ta wucin gadi ce.

Wannan shi en karo na biyu da shugaba Obama ke dage zirar da shirya kaiwa Indonesia da Australia. A watan Maris ma an dage wannan zira, lokacin da shugaban ke neman majalisun dokokin kasar su a amince da kudurinsa na kiwon lafiya.