Obama ya sake ziyartar yankin da mai ke malala cikin tekun Mexico

Shugaba Obama a yankin da mai ke malala a tekun Mexico
Image caption Shugaba Obama a yankin da mai ke malala a tekun Mexico

Fiye da makwanni shida bayan da mai yayi ta kwarara a tekun Mexico daga wata rijiyar mai, Injiniyoyi sun yi nasarar karkatarda wani bangaren Man da ke ta kwarara zuwa cikin wasu jiragen ruwa dake cikin tekun.

Tuni dai Shugaba Obama ya ziyarci yankin da kwararar man ta shafa, domin ganewa idanunsu irin barnar da Man yayi, inda yace ran shi ya baci ainun akan kamfanin da alhakin wannan abu ya rataya a wuyansa.

Ziyarar, wadda ita ce ta ukku tun lokacin da aka fuskanci matsalar, ta zo ne a yayin da ran jamaa ke ci gaba da baci a Amurka.

Kamfanin Mai na BP, ya ce a karshe dai ya samu ci gaba wajen kokarin dode bakin rijiyar, sai dai ya ce ana bukatara karin sa'oi 48 kafin a sani ko matakin mai dorewa ne.

Sai dai a nasa bangaren, shugaba Obama ya ce: "ya yi wuri a yi tsammanin samun nasara".

Editan BBC na yankin arewacin Amurka Mark mardell, ya ce tsiyayar man na ci gaba da tayar da kurar siyasa a kasar, kuma ziyarar shugaba Obama, wani bangare ne na kokarin da gwamnatinsa ke yi na kaucewa sukar da ake yi mata dangane da yadda take tunkarar batun tsiyayar man.