Isra'ila na binciken jirgin ruwan kai agaji Gaza

Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa
Image caption Har yanzu agaji bai kai Gaza ba

Isra'ila ta karkata akalar wani jirgin ruwan Jumhuriyar Ireland da ke kokarin kai kayan agaji zuwa yankin Gaza, wanda Isra'ilan ta killace.

Sojin Isra'ila da suka suka shiga cikin jirgin, kusan kilomita 30 daga gabar ruwan Gaza, sun ce ba su fuskanci wata turjiya ba, kuma an tafi da jirgin zuwa tashar jiragen ruwa ta Ashdod.

'Yan sandan Isra'ila suna binciken jirgin, tare da yin tambayoyi ga ma'aikatan jirgin da kuma masu goyon bayan Falasdinawa su 11 dake cikinsa.

Jirgin ruwan dai mai suna Rachel Corrie, shi ne na bakwai a jerin jiragen da sojin Israila suka kama tun ranar Litinin, inda suka kashe mutane akalla 9.

Babu dai wata musayar bayanai da aka yi da masu goyon Palesdinawan da ke cikin jirgin ruwa na Rachel Corrie.