An yi kade-kaden neman agaji a Mali

Taswirar kasar Mali
Image caption Arewacin kasar Mali na fama da matsanancin fari

An gudanar da wani taron kade-kade da raye-raye a Bamako, babban birnin kasar Mali, don tara kudaden agaji ga mutanen da matsanancin fari ya shafa a arewacin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane dubu dari biyu da hamsin ne ke karbar agajin abinci yanzu haka a kasar.

Shahararriyar kungiyar mawaka da makadan nan ta buzaye mai suna Tinariwen na cikin kungiyoyin mawakan da suka cashe a wajen taron kade-kade da raye-rayen na Bamako.

Wasu jama'a ne dai daga arewacin kasar suka shirya wannan taro.

Babbar sana'ar mutanen yankin arewacin Mali dai ita ce kiwon shanu; a halin da ake ciki kuma an kiyasta cewa kashi tamanin cikin dari na shanun na fama da karancin abinci.

Mutuwar shanun dai kan kawo karancin kudi a hannun mutanen yankin, al'amarin da kan sa samar da abinci ga iyalai ya yi wahala.

Su ma 'yan kungiyar ta Tinariwen mutanen arewacin kasar ne wadanda suka yi suna a sassa daban daban na duniya.

Kungiyar dai kan kwashe kwanaki da dama tana yawon kade-kade da wake-wake a kasashen duniya to amma, a cewar daya daga cikin ‘ya’yanta, Abdallah Ag Alhousseyni, ta damu matuka da halin da ake ciki.

“Gaba daya iyali na makiyaya ne; kuma ko da yake na gina gida a garin Kidal, kashi casa'in cikin dari na iyali na a cikin hamada suke suna kiwo.

“Su ma wannan matsala ta shafe su”, inji Alhousseyni.

Gwamnatin Mali ta bayyana cewa tana rarraba abinci ga mutanen yankin da abin ya shafa da ma dabbobinsu.

To amma kungiyoyin makiyayan sun ce abin da gwamnatin ke yi bai wadatar ba, don haka kungiyoyin kasa-da-kasa ke kira da a kara yawan agaji ga yankin.

Wadanda suka shirya taron dai sun ce an tara kimanin dala dubu arba’in a lokacin kade-kaden da wake-waken.