Za a kwashe kasar kauyuka biyar a Najeriya

inda ake hakar zinare a Najeriya
Image caption Yara dari da sittin da uku ne suka mutu a kauyukan da ake hakar zinare ba bisa ka'ida ba

Hukumomin jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun ce daga gobe Litinin ne za su fara aikin debe kasar wasu kauyuka biyar da ke yammacin jihar, a wani bangare na kokarin shawo kan mace-mace da nakasar mutane, musamman yara, a wadannan kauyukkan sakamakon shaka ko hadiyar gubar dalma dake fitowa daga wasu wuraren hakar zinare.

Wata cibiya mai yin ayyukan da suka shafi muhalli, wadda kuma ita za ta yi aikin kawar da gubar dalmar, ta shaidawa BBC cewa karin wasu daruruwan yaran kanana za su iya mutuwa sakamakon mu'amala da dalmar mai guba.

Shugaban cibiyar mai suna Blacksmith Institute, Richard Fuller, ya ce saboda jinin yawancin yaran cike yake da gubar dalmar, za su iya rasa rayukansu nan da wani lokaci.

A ranar Juma'a ne dai hukumomin kiwon lafiya a Najeriya suka tabbatar da mutuwar yara dari da sittin da uku sakamakon shaka ko hadiye gubar a wadannan kauyukan inda ake hakar zinare ba bisa ka'ida ba.