Kowa zai ji a jikinsa-inji Cameron

David Cameron da mataimakinsa Nick Clegg
Image caption David Cameron da mataimakinsa Nick Clegg sun sha alwashin kawo sauyi

Fira Ministan Burtaniya David Cameron, yayi gargadin cewa za a fuskanci kalubale ta fuskar biyan albashi da fansho da sauran albarkatun aiki, a sauye-sauyen da gwamnati ke shirin bullowa da su.

A wani jawabi da yayi, yace shawo kan matsalar gibin da kasar ke mafa da shi, abune da zai shafi "rayuwar kowa da kowa".

Ya kara cewa matsalolin "sun fi yadda aka zata muni" sannan ya daura alhakin matsalar ga gwamnatin Labour data gabata.

Idan har ba a dauki mataki ba, a cewarsa Burtaniya za ta dinga biyan fan biliyan 70, a matsayin kudin ruwa kan basukan ta daga shekara ta 2015.

Matse bakin aljihu

Sai dai yace ba zai rage kudaden da ake kashewa "ta yadda zai yi illa ga wadanda ke bukatar taimako ba" ko kuma yadda zai kawo rabuwar kawuna a kasar ba".

Gwamnatin hadin gwuiwar kasar ta sha alwashin rage abinda ake kashewa da fan biliyan 6.2 a bana-abinda 'ya'yan jam'iyyar Lib Dems suka soka a lokacin yakin neman zabe.

Sai dai jam'iyyar adawa ta Labour ta soki matakin tana mai cewa aiwatar da shi cikin gaggawa zai iya jefa yunkurin farfado da tattalin arzikin kasar cikin rudani.

Daya daga cikin masu neman shugabancin jam'iyyar Labour David Miliband, ya zargi shugaban jam'iyyar Lib Dems Nick Clegg da munafurci.

"Tsauraran matakai"

"Wannan wanne irin almubazzaranci ne..... Wannan shi ne darasin da muke so mubar wa 'yar baya," a cewarsa.

Mista Cameron yace matakin ya zama wajibi, yace ina fatan wannan gwamnatin ta kawar da gibin da Burtaniya ke fama da shi, tare da hada kawunan 'yan kasar.

Sai dai shugaban yace zai kare kudaden da ake kashewa a harkar lafiya da kuma taimakon kasashen waje.

Sai dai Hugh Lanning, mataimakin sakataren kungiyar ma'aikatan kudi dana gwamnati, ya gayawa BBC cewa bankuna da rikicin tattalin arziki su ne suka haifar da matsalar bawai ma'aikatan gwamnati ba.