Kakakin sojin Nijar ya ziyarci Da`koro

Nijar
Image caption Wani yaro mai fama da ciwon tamowa

A Jamhuriyar Nijar Kakakin Majalisar mulkin sojin `kasar Kanal AbdulKarim Goukoye, ya kai wata ziyarar gani da ido a Gadabeji na yankin Da`koro a jihar Mradi

Ana dai ganin cewa yankin Da'akoro shine ya yafi fama da matsalar `karancin abincin a jahar Maradi .

Tuni dai ake ta rade radin cewa yanzu haka dabbobi da dama ne ke mutuwa a wannan yanki sakamakon matsalar yunwa da ake fama da ita..

Baya ga haka kuma wasu yan kasar na fama ciwon tamowa sakamakon karancin abinci

Wakiliyar BBC ta ce Hukomomin kasar sun kaima mazauna yankin abinci wanda za'a tsayar masu cikin farashi mai rahusa