Hukunci kan rikicin shugabancin jam'iyyar MNSD-Nasara

Taswirar Jumhuriyar Nijer
Image caption Taswirar Jumhuriyar Nijer

A jamhuriyar Niger yau kotun daukaka karar a birnin Yamai ta bada sakamakon wata sharia a tsakanin Malam Hama Amadu tsohon shugaban gwamnatin Niger da malam Seini Umaru, shi ma tsohon shugaban gwamnatin kasar.

Hukuncin dai dai ya ce daga yau, malam Seini Umaru ne shugaban jamiyyar ta MNSD Nassara.

Tuni dai Hama Amadun ya ce ya amince da wannan hukunci, kuma ya ma fice daga jam'iyyar don shiga sabuwar jam'iyyar MODEM-Lumana.

Takaddama a kan shugabancin jamiyyar ta MNSD-Nasara dai ta samo asali ne a bara, bayan da wani babban taron Congres na jamiyyar da aka yi a birnin Damagaram ya sauke Malam Hama Amadu daga jagorancinta ,tare da zaben Malam Seini Umaru, wanda shi ne Fira minista a lokacin, don ya shugabanci jam'iyyar.