Obama ya maida martani kan tekun Mexico

America
Image caption Shugaba Obama

Shugaba obama ya maida da martani kan masu sukar sa

Shugaban Amurka Barack Obama ya kare matakan da gwamnatinsa ta dauka dangane da batun tekun mexico.

Hakan ya biyo bayan cewa wasu na sukarsa kan cewa ya gaza wajen daukar matakan da suka dace wajen shawo kan man da ya rika tsiyaya a tekun Mexico.

Sai shugaban Amurkan ya ce, zai kori shugaban kamfani mai na BP Tony Horward daga aiki, wanda ake sukar sa a kasar kan halin ko in kula da ya nuna, akan illar dake tattare da wannan lamari.

Buggu da kari, ya ce zai dau tsauraran matakai kan kamfanonin mai, kuma zai rika sa ido akan yadda suke gudunar da ayyukansu.

Shugban ya fadama wani gidan talibinjin cewa, tun farko ya kasance a ainihin wurin da abun ya faru inda ya tattaunawa da wadanda abun ya fi shafa, kan irin illar dake tattare da wanan lamari, tun kafin masu sharhi kan lamura sun fara tsokaci kan batun

Wakilin BBC ya ce, alamu na nuni da cewa ,ana samun nasara dangane da matakin baya baya nan da kamfanin mai na BP ya dauka, ta hanyar amfani da wata naura dake debar yawan man da kamafanin ya ce yana tsiyaya a kowace rana .

Sai dai kuma man dake saman teku, ya kasu gida gida abun da kuma zai kawo cikas ga shirin tsaftace tekun.