An kafa cibiyoyin tafi da gidanka a Zamfara

Wasu rumbunan ajiye abinci a Zamfara
Image caption Wasu rumbunan ajiye abinci a jihar Zamfara

Rahotannin da ke fitowa daga Jihar Zamfara inda jama'a suka shaki gubar dalma, sunce ma'aikatan kiwon lafiya sun kafa cibiyoyin tafi da gidanka, domin yiwa yaran da wannan abu ya shafa magunguna.

Rahotannin sun ce gubar ta shafi ruwan shan da mutane ke amfani da shi ne a kauyuka shidda a Jihar ta Zamfara, kauyukan dake gaba da wurin da ake hakar lu'u-lu'u.

Wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza, ya yi tattaki zuwa babban asibitin Bukuyum, inda aka kafa sansanin da ake yiwa yaran da wannan abu ya shafa magunguna.

Ya ce jama'a da dama sun fito domin samun magani.

Ya kara da cewa yaga yara da dama kwance a cibiyoyin, yayinda wasu ke zaune cikin koshin lafiya, wasu na fama da cutar sosai.

Fiye da mutane 350 aka rawaito cewa sun kamu da cutar a watannin da suka gabata, kuma 111 daga cikin wadanda suka rasu yara ne, wadanda shekarun su basu haura biyar ba.

Sai dai ma'aikatar lafiya ta gwamnatin tarayyar kasar ta ce ta shawo kan lamarin.

Dauki

Najeriya dai ta nemi dauki daga kasashen duniya, wadanda suka hada da Hukumar Lafiya ta Duniya da Cibiyar kawar da cututtuka ta Amurka.

Har ila yau akwai Cibiyar yaki da gurbata yanayi ta Blacksmith Institute da ke New York.

Wakilin BBC ya ce jami'an Amurka na bi gida-gida domin suna zakulo mutanen dake fama da cutar.

Haka kuma tawagar likitoci daga kasar Holland wadanda ke aiki a Arewacin Najeriya, sun kawo magunguna na musamman domin kai dauki ga yaran da jinin su ya hau.

Kwanaki 28

Dakta Nasir Sani-Gwarzo, daya daga cikin jami'an da ke shirya aikin ceton, ya ce an kai dauki ga kauyukan, kuma anyi awangaba da wadanda abin ya shafa zuwa cibiyoyin bada magani.

Ya kara da cewa za a ajiye su a wurin har na tsawon kwanaki 28.

"Sun yi kokarin tantance wadanda annobar tafi shafa, ta hanyar gano ainahin matsalar," a hirar sa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Yace hukumomi da kananan hukumomi na jihar Zamfara da ma'aikatar lafiya ta kasa, duk sun hada kai wajen samar da agaji ga wadanda abin ya shafa.

Tare da tsaftace gidaje a kauyukan da abin ya shafa, da wayar da kan jama'a kafin saukar damunar bana.

A yanzu gwamnatin jihar tace ta ware dala naira miliyan 240 domin aimakawa wajen shawo kan matsalar.