Kura ta lafa a rikicin da faru a jinar Borno

Rikici
Image caption Wani wanda ake jinyar sa a asibiti sakamakon rauni da ya samu

Mutane goma sun sami raunuka a jihar Borno

Rahotanni daga jihar Borno dake Arewacin Najeriya na nuni da cewar kimanin mutane goma ne yanzu haka, ke kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka samu a rikicin daya barke, tsakanin yan kabilar Margi da Koyam, a kauyen Shettima Abogu dake karamar Hukumar Damboa.

Rundunar yan sandar jihar Borno ta tabbatar da abkuwar wannan rikici, da cewar ya faru ne a sakamakon wasu filayen noma da tun a bara ake takaddama akai tsakanin bangarorin biyu.

kwamishan yansanda jihar mallam Ibrahim Audu ya fadama BBC cewa, an tsaurara matakan tsaro a wannan kauye, dama wasu kauyukan dake kusa domin gudun sake abkuwar rikicin.

A baya dai jihar Borno ta fuskanci tashe tashen hankula, a lokacin da yan kungiyar Boko Haram sukayi ta artabu da jami'an tsaron kasar.

Lamarin a wanan lokaci, ya janyo asarar dukiyoyi da kuma rayukan mutane.