An cafke hodar iblis mai yawa a Gambiya

Hodar iblis ta cocaine da aka kama a Gambiya
Bayanan hoto,

Safarar miyagun kwayoyi a Afrika na neman gagarar kundila.

Hukumomi a Kasar Gambiya dake yankin yammacin Afrika sun kwace hodar iblis ta cocaine, wadda darajarta ta kai ta fiye da dola biliyan daya, tare da taimakon masu bincike na Birtaniya.

Tan biyu da rabi na cocaine ne aka samu a wani dakin ajiya dake kusa da Banjul babban birnin kasar.

An kama mutane sha biyu da ake kyautata zaton 'yan asalin Latin Amurka da Turai da yammacin Afrika ne, sannan kuma an kwace tarin kudi, da kuma makamai da bayanan Kwamputa.

Kamen ya zo ne yayinda kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi a yankin latin Amurka ke ci gaba da yin amfani da yankin yammacin Afrika a matsayin wata hanyar safarar hodar Cocaine zuwa Turai.