Goodluck ya amince da Jega a matsayin shugaban INEC

Farfesa Jega
Image caption Attahiru Jega ya dade yana gwagwar maya a fannoni da dama a Najeriya

Majalisar kasa a Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasa Goodluck Jonathan na nadin Farfesa Attahiru Jega a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaben kasar.

Hakan dai zai baiwa shugaban damar nada Farfesa Jega a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta kasar.

Majalisar wacce ta hada da tsaffin shugabannin kasar da gwamnoni masu ci da shugabannin majalisar dokoki ta kasa, sun amince da nadin nasa ne bayan wani taro da suka gudanar a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.

Duka tsaffin shugabannin kasar ne dai suka halacci taron majalisar.

Wakilin BBC Ibrahim Isa, yace mai yiwuwa wannan nadin ya kwantarwa da 'yan kasar hankali, ganin irin kyawun zaton da ake yiwa Attahiru Jega, wajen aiwatar da gaskiya.

Sai dai acewar Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC, har yanzu akwai sauran aiki a gaban 'yan kasar, wajen fitowa domin yin rijista da kuma kare kuri'unsu.

A yanzu dai ya ragewa majalisar dattawan kasar ta amince da nadin nasa, sannan a rantsar da shi domin fara aiki. Dama dai anta rade-radin cewa za a baiwa Malam Jega wannan matsayi a kafafen yada labarai na kasar.

Farfesa Jega

Farfesa Jega dai shi ne shugaban Jami'ar Bayero da ke Kano, wanda kuma masu sharhi ke kallon ya taka rawa sosai wajen farfado da jami'ar.

Ya kuma taba zamowa shugaban kungiyar malaman jami'o'in kasar wato ASUU.

Yana daya daga cikin 'yan kwamitin mai shari'a Lawal Uwaisu, wanda ya gabatar da gyra-gyaren da za a yiwa tsarin mulkin kasar.

Ya yi karatu a jami'ar Ahamadu Bello University, sannan yaje Amurka, inda ya samu digiri na biyu da na uku.

Ya kuma shugabanci sashin kimiyyar siyasa na jami'ar Bayero da ke Kano.

A watan Oktoba mai zuwa new ake saran wa'adin sa zai kare kan shugabancin jami'ar ta Bayero.

Kalubale

A kwai dai babban kalubale a gaban sabon shugaban hukumar da ake saran nadawa.

Ganin irin matsalolin da suke tattare da harkar zabe a kasar.

Abaya dai anzargi jami'an hukumar zaben kasar, da gazawa wajen shirya zabuka masu inganci a kasar.

A shekara ta 2007, kasashen duniya sun yi Allah wadai da kasar, bayan da ta gudanar da zaben bayyana a matsayin mafi muni a tarihi tun da kasar ta samu 'yan cin kai.

A yanzu ya rage kasa da shekara guda ne kawai kafin 'yan kasar su koma rumfunan kada kuri'a domin zaben kasa baki daya.

Kuma alamu na nuna cewa zaben zai zamo daya daga cikin mafiya mahimmanci a tarihin kasar.

Wasu na ganin damace a gareshi ta aiwatar da shawarwarin da suka gabatar a kwamitin mai shari'a Lawal Uwaisu.