Mutane bakwai sun halaka a Pakistan

Pakistan
Image caption Wata tankar kungiyar NATO bayan da wasu yan bindiga suka smata wuta a Pakistan

An bude ma dakarun kungiyar NATO wuta

Wasu yan bindiga sun bude wuta kan dakarun kungiyar kawance ta NATO a Islamabad, babban birnin Pakistan inda suka kashe akalla mutane bakwai, tare da kona wasu motoci da dama inda daga bisani yan bindigan suka tsere.

Wakiliyar BBC ta ce jerin gwano motocin masu dauke da kayayakin kungiyar kawance ta nato wadanda ke kan hanyar zuwa Afghanistan na fuskantar hari akai akai daga hanun yan bindiga dake wanan wuri.

Sai dai wannan shine karon na farko da za'a kai hari kusa da babban birnin kasar inda ake da matukar tsaro.

Hukomomin yan sanda sunce wadanda suka kai harin na dauke ne da manyan makamai hade da bama bamai

Sun kuma ce yan bindigan da suka gudunar da wannan aiki, sun kai su goma sha biyu wadanda ke rike da bindigogi, da kuma bama bamai.

Daga farko dai sun bude ma mottocin wuta da bindigar su sannan kuma suka kona motocin.

Mayakan kungiyar kawance ta NATO dake Afghanistan sun dogara ne kan iyakar Pakistan wajen shigowa da kayayaki, sai dai manyan kwamadojin kungiyar sun ce sun fara neman wata sabuwar hanyar bi.