Hanyar jirgin kasa mafi sauri a Afrika

Jirgin kasa mafi sauri a nahiyar Afrika
Image caption Jirgin kasa mafi sauri a nahiyar Afrika

An bude hanyar jirgin kasa mafi sauri a nahiyar Afrika, a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.

Hanyar ta Gautrain, wacce keda saurin kilo mita160 a sa'a guda, na daukar matafiya tsakanin filin saukar jiragen sama na Oliver Tambo da birnin Johannesburg.

A dai dai lokacin da ake fara gasar cin kofin duniya, ana saran fiye da baki 30,000 ne za su halarci kasar domin gasar wacce za a shafe wata guda anayi.

Sabowar hanyar dogon za ta dauki bakin zuwa cikin gari a mintuna 15, tafiyar da kan dauki fiye da sa'a guda a karamar mota.

Sai dai kwangilar aikin wacce ta ta samma dala biliyan uku, ta fuskanci kalubale da dama tun bayan farata kimanin shekaru hudu da suka wuce.

Wakilin BBC Jonah Fisher, yace jama'a da dama sun soki shirin ganin cewa gwamnati ce ta biya mafiya yawan kudin aikin.

Masu sukar aikin na fakewa da dimbin 'yan kasar ta Afrika ta Kudu da ke fama da talauci.

Ana saran fadada hanyar jirgin domin ta hada da kananan unguwanni a nan gaba.