Ma'aikata sun fara yajin aiki a Spaniya

Ma'aikata na yajin aiki a Spain
Image caption Ma'aikatan na adawa da zaftare musu albashi da gwamnatin zatayi.

Ma'ikatan gwamnati a Spain sun fara wani yajin aiki domin nuna adawa da yanke kimanin kashi biyar na albashinsu da za'a fara daga farkon wannan watan.

Ma'aikatan sun shirya wata zanga zanga a gaban ma'aikatar lura da tattalin arziki.

Wannan mataki da gwamnatin ta Spain ta dauka zai zama wani gwaji gareta na matakan tsuke bakin aljihu da take dauka.

Daya daga cikin kungiyar kwadagon dake jagorantar yajin aikin ta bayyana cewa ma'aikata kimanin kashi 75 cikin dari sun daina zuwa aiki a duk fadin kasar.