Kungiyar Amnesty ta soki gwamnatin Pakistan

Tambarin Kungiyar Amnesty
Image caption Rahotan Kungiyar Amnesty dangane da Pakistan ya soki gwamantin kasar

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International tayi kira ga 'yan Taliban da kuma gwamnatin kasar Pakistan da su kawo karshen cin zarafin bil'adama a yankin arewa maso yammacin kasar.

Wani sabon rahoto da kungiyar ta fitar, yace halinda mutane ke ciki a wannan yanki ya ta'azzara a 'yan shekarun nan, yayinda ikon 'yan Taliban ke karuwa.

Kungiyar tace akwai alamun dake nuni da cewar gwamanti tana nuna halin ko in kula a yankin.

Kungiyar ta Amnesty dai ta bayyana abinda fararen hula da dama a wannan yanki suke tsoron fitowa fili su fada.

Amnesty ta zargi 'yan Taliban dake wannan yanki da cin zarafin fararen hula da aikata kisa da kuma farma malaman makaranta da kuma ma'aikatan agaji

Rahotan na Amnesty ya kuma zargi dakarun kasar Pakistan da cewar sun gaza wajen baiwa fararen hula kariya haka kuma gwamnatin kasar bata bayarda cikakkiyar kulawar daya kamata dangane da samar da ababen more rayuwa a yankin