A yau Ban ki Moon zai ziyarci Burundi

Ban ki Moon zai ziyarci Burundi a yau

A yau laraba ne ake saran babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Banki Moon zai isa `kasar Burundi

Sakatare janarar din zai ziyararci kasar ne da zimmar, karfafa guiwar dakarun kasar wadanda ke cikin rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar Somalia.

Kasar ta Burundi dai na da fiye da dakaru dubu biyu a rundunar wanzar da zaman lafiyar na majilisar dinkin duniya tun daga shekaru uku da suka gabata wadanda kuma wasu da dama daga cikin su suka rasa rayukan su.