Iran tayi watsi da takunkumin da aka sa mata

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad
Image caption Shugaba Mahmoud Ahmadinejad

Kasar Iran ta yi fatali da karin takunkumin da kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya ya kakaba mata, dangane da shirinta na makamashin nukiliya.

Shugaban kasar Iran din Mahmoud Ahmadinejad, ya bayyana matakin da cewa ba shi da wani tasiri, kuma ya ce kamata yayi a yasar da shi a kwandon shara kamar tsimman da aka gama amfani da shi. Kasar Iran din ta kuma lashi takobinm cigaba da shirinnata.

Kasashen Turkiya da Brazil suma sunyi allawadai da takunkumin suna masu cewar maiyiwuwa ya rufe kofofin tattaunawar da dama can suke a bude. Brazil da Turkiya dai sun kada kuriar amincewa da karin sabbin takunkumin tunda farko.

Manyan kassahen dai sun kara da cewar wannan wani takunkumi ne mafi tsauri da kasar Iran ta taba fuskanta, kuma kasasahen suna da goyan bayan wasu kassahen duniya da dama

Kuri'ar da aka kada dai tayi nuni da cewar akwai rarrabuwar kai tsakanin kassahen dake cikin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.

Kasar Amurka wacce ita ce ta matsa don ganin cewar an sanyawa Iran din karin takunkumi, tayi ikirarin samun nasara ta diplomaciya