Jam'iyyar RDP ta yi na'am da dokar cire kariya

Salou Djibo
Image caption Shugaban mulkin sojin Nijar, Salou Djibo

A jamhuriyar Nijar, jam'iyar RDP Jama'a ta yi marhabin da tanajin sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Shi dai sabon kundin ya soke wani sashe da ya bada kariya ga wadanda ake zargi da aikata kisan gilla ga tsohon shugaban kasar Janar Ba'are Mainasara a 1999.

Da ma dai jam'iyyar ta RDP ta dade tana gwagwarmayar ganin an soke wannan afuwa.

Kodayake dai, wannan mataki ba zai tabbata ba, sai bayan an kada zaben raba-gardama kan sabon kundin tsarin mulkin.

Alhaji Sani Abdurrahman, babban sakatare jam'iyyar RDP Jama'a; ya shaidawa Wakilin BBC Idy Baraou, cewa yana fatan ganin sabon tsarin ya tabbata.

Sannan ya ce basu da shakku game da cewa kudurin zai samu karbuwa a wajen jama'ar kasar idan aka zo kada kuri'a.