Kungiyoyin kare hakkin jama'a sun gana da Mamadou Tanja

Malam Mamadou Tanja
Image caption Malam Mamadou Tanja

Wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam a Niger sun ziyarci tsohon shugaban kasar da sojoji suka hambarar, Malam Mamadou Tanja, da tsohon ministan cikin gida Malam Albade Abouba, a wurin da ake tsare da su, tun bayan juyin mulkin watan Fabrairun da ya wuce.

A cikin hira da BBC, Malam Khalid Ikiri, shugaban kungiyar ANDDHA, ya ce mutanen biyu suna cikin koshin lafiya, ba su da wata damuwa, illa dai ta jiran a sake su.

Kungiyoyin sun jaddada kiran da suka yi na a saki mutanen biyu, idan hukumomin shari'a sun tabbatar ba su aikata wani laifi ba.